15 Oktoba 2026 - 17:14
Source: ABNA24
Yamen: Harba Makami Mai Linzami Zuwa Madina Munawwara Ƙarya Ce Tsantsarta

Saudiyawa sun sake maimaita iƙirarin harba makami mai linzami daga Yemen zuwa birnin Madina Munawwara wanda Yemen nan take ta ƙaryata wannan iƙirarin kuma ta kira shi ƙarya tsantsa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sojin Saudiyya sun sake maimaita iƙirarin harba makami mai linzami daga Yemen zuwa birnin Madina Munawwara wanda Yemen nan take ta ƙaryata wannan iƙirarin kuma ta kira shi ƙarya tsantsa.

Mintuna kaɗan da suka wuce Saudiyya ta yi iƙirarin kakkabo wani makami mai linzami na cruise a Madina Munawwara; amma nan take mai magana da yawun sojojin Yemen a cikin wani gajeren saƙo ya bayyana cewa sojojin Yemen a yau ba su yi wani harbin makami mai linzami zuwa Saudiyya ba.

Birgediya Yahya Saree game da wannan ya bayyana: sojojin Yemen suna nanata cewa a yau ba su gudanar da wani aiki zuwa ƙasar Saudiyya ba kuma iƙirarin maƙiya Saudiyya na kai hari wajen Madina Munawwara, ƙarya ce babba kuma ƙiren ƙarya bayyanan ne.

..........................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha